Ko shakka babu akwai sauran taƙaddama a makomar ɗan wasan gaban Real Madrid Vinicius Jr.
Dan wasan wanda babu ja yana cikin 'yan wasan kwallon ƙafa na duniya mafiya shahara gobensa ba ta bayyana ba ya zuwa yanzu.
Dan Brazil ɗin zai shiga shekaarsa ta ƙarshe ne a kwantaraginsa da ƙungiyar ta Sifaniya, kuma irin waɗannan 'yan wasa ba a barin kwantaraginsu ta kai irin wannan lokaci ba tare da tsawaita ta ba.
Ya koma Madrid ne yana da shekara 18 a 2018, ya ci kwafuna 14 ya zura kwallo 128 a wasa 375 da ya yi a ƙungiyar tasa.
Rahotanni daga kasuwar saye da sayerwar 'yan wasan Turai na cewa darajar ɗan wasan za ta kai £200m.
Madrid ta yi yunƙurin sabunta kwantaragin ɗan wasan ko kuma fara magana kan makomarsa ranar Litinin ɗin nan, sai dai har yanzu babu wata magana mai kwari kan hakan.
Tuni Arsenal suka nuna muradinsu kan ɗan wasan, wanda wasu ƙungiyoyin Saudiyya suka riƙa nuna muradinsu kan shi.
Kocin Gunners Mikel Arteta ya jima na son ɗaukar ɗan wasan da zai buga masa ɓangaren hagu wanda ya nuna kansa, kuma Vinicius ya nuna cancantarsa kan zaɓin.
Tun bayan da ta rasa ɗan wasan da ta so ɗauka Morgan Rogers da Chelsea ta saya, Arsenal ta ƙara matsa ƙaimi kan ɗaukar ɗan wasan.