Cikin watan Agusta za a fara gasar wasanni musamman a nahiyar Turai, kenan wannan dama ce ta ƙungiyoyi su yi cefane kafin a bude labulen wasannin bana 2026/27.
Ga wasu labaran da suka shafi kasuwar cikikayyar yan kwallon
Romero na dab da barin Tottenham
A cewar talkSPORT, alamu na nuna cewa ƙyaftin din Tottenham, Cristian Romero, na dab da barin kungiyar ta Arewacin Landan.
Dan wasan tawagar Argentina mai shekara 28 ya tattauna da zakarun Serie A na Italiya, Inter Milan, a kwanakin baya. Sai dai rahotanni sun ce burinsa shi ne ya koma buga gasar La Liga ta Sifaniya, inda ake rade-radin cewa Barcelona na sha'awar sayensa.
Arsenal na sauraron Julian Alvarez
Rahoton talkSPORT ya bayyana cewa Arsenal na duba yiwuwar daukar dan wasan gaba na Argentina, Julian Alvarez, a wannan bazarar.
An ce Alvarez mai shekaru 26 ya sanar da Atletico Madrid cewa yana son barin kungiyar. Duk da haka, ana ganin Barcelona ce kungiyar da ya fi sha'awar komawa.
Roma na neman Crysencio Summerville
Jaridar Corriere dello Sport ta ruwaito cewa wakilan dan wasan tawagar Netherlands, Crysencio Summerville, sun gana da kungiyar Roma domin tattauna yiwuwar komawarsa Italiya.
Summerville mai shekaru 24 na wasa ne a West Ham United, wadda ta fadi zuwa gasar Championship bayan kakar wasan da ta gabata.
Mason Greenwood Ya Koma Fenerbahce
Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ta tabbatar da daukar dan wasan gaba Mason Greenwood daga Marseille kan kwantiragin shekara hudu.
An kammala cinikin ne kan Yuro miliyan 39 (kimanin Fam miliyan 33.25), wanda za a biya sau uku a tsawon shekaru uku.
Tun bayan komawarsa Marseille daga Manchester United a watan Yulin 2024, Greenwood ya zura kwallaye 48 a wasanni 81. A kakar da ta gabata, shi ne na biyu a jerin masu yawan cin kwallaye a Ligue 1 bayan Esteban Lepaul na Rennes.
Ana sa ran zai fara buga wasa a sabuwar kungiyarsa a karawar neman gurbin shiga Champions League da Gornik Zabrze mako mai zuwa.
Harry Winks ya koma Cagliari
Tsohon dan wasan Tottenham da tawagar Ingila, Harry Winks, ya koma kungiyar Cagliari ta Italiya daga Leicester City.
Dan wasan mai shekara 30 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu da kungiyar Serie A.
Winks ya shafe shekaru uku a Leicester, inda ya taimaka mata ta samu haurowa zuwa Premier League, kafin daga bisani kungiyar ta fuskanci faduwa daga gasar sau biyu a jere.
Ya buga wasanni 109 a Leicester tare da zura kwallaye biyar da bayar da taimakon kwallo guda biyar.
Sunderland ta ɗauki Thomas Meunier
Sunderland ta sanar da daukar dan wasan Belgium, Thomas Meunier, kan kwantiragin shekara biyu.
Dan wasan mai shekara 34 ya zo ne bayan karewar kwantiraginsa da Lille, inda ya buga was 81.
Meunier ya wakilci Belgium sau uku a gasar cin kofin duniya ta bana kafin Spain ta fitar da kasarsa a wasan kwata-fainal.
Lewis Dobbin ya koma Southampton
Southampton ta kammala daukar dan wasan gaba, Lewis Dobbin daga Aston Villa a yarjejeniyar da aka ce ta kai kusan Fam miliyan 10.
Dan wasan mai shekaru 23, wanda ya shafe kakar wasan da ta gabata aro a Preston North End, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru hudu da Southampton.