Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Sojin Najeriya sun ceto mutum 48 da aka sace a Zamfara

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutum 48 da aka yi garkuwa da su bayan da suka kai ɗauki cikin gaggawa sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan ta’adda suka kai.

    Ƴan ta'addan sun kai harin ne a ƙauyen Magami da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara da sanyin safiyar ranar 26 ga Yulin 2026.

    Sai dai mutum ɗaya ya rasa mutu a harin, yayin da wasu mutum biyu suka samu raunukan harbin bindiga, inda aka kai su asibitin ƙwararru na Kaura Namoda domin samun kulawar likitoci.

    A cikin sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce sojojin sun samu kiran neman taimako ne bayan wasu mahara masu yawa da ke kan babura 40 suka mamaye ƙauyen, inda suka tattara mazauna yankin da nufin tafiya da su cikin daji.

    A yayin da sojojin suka isa wurin, suka fafata da maharan, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigar yin watsi da mutanen da suka sace tare da tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

    Rundunar ta ce wannan mataki ya ba da damar kuɓutar da dukkan mutum 48 da aka yi garkuwa da su.

    Ta kuma ƙara da cewa sojojin sun ci gaba da sintiri a yankin domin hana sake aukuwar makamancin wannan hari da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

  2. Iran ta yi allawadai da harin jirgin ruwanta inda ta kuma gargaɗi Ukraine

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka ga Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, bayan harin jirgin ruwan kasuwancin Iran da aka kai da jirgin marar matuki a Tekun Caspian, yana mai cewa harin ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.

    A wani sako da ya wallafa a shafin X, Araghchi ya ce harin ya yi sanadin mutuwar wani ma’aikacin jirgin, kuma ya zargi Ukraine da aikata abin da ya kira take dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

    Ya kuma bayyana cewa ya tattauna batun da babbar jami’ar harkokin wajen Tarayyar Turai, Kaja Kallas, da kuma Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov.

    A nasa ɓangaren, Lavrov ya jajanta wa Iran kan mutuwar ma’aikacin jirgin, tare da jaddada buƙatar dakatar da irin waɗannan hare-hare.

  3. Sojojin Lebanon sun yi allawadai da ci gaba da hare-haren Isra’ila a Kudancin ƙasar

    Sojojin Lebanon sun yi allawadai da ci gaba da hare-haren sojojin Isra’ila a kudancin ƙasar, suna masu cewa waɗannan hare-haren na hana su kammala tura dakarunsu kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma da Isra’ila a watan da ya gabata ta tanada.

    A wata sanarwa da rundunar sojin Lebanon ta fitar, ta ce sojojin Isra’ila na ci gaba da ƙeta yarjejeniyoyi da dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar rusa gidaje da kai hare-haren bama-bamai da kuma harbe-harbe da manyan bindigogi a yankuna daban-daban na kudancin Lebanon.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ci gaba da waɗannan hare-hare ya kawo cikas ga tura sojojin Lebanon bisa yarjejeniyar da aka amince da ita, tare da hana mazauna yankunan da abin ya shafa komawa garuruwansu da ƙauyukansu.

  4. Babban jami'in kuɗi na ƙungiyar ISWAP ya miƙa wuya - Sojojin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa wani babban jami’in da ke kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar ISWAP ya miƙa wuya ga dakarunta a wani sabon ci gaba da ke nuna ƙara raunana ƙungiyar a yankin Arewa maso Gabas.

    Rundunar ta kuma ce kimanin mayaƙa 46 tare da iyalansu sun miƙa wuya a kwanakin baya-bayan nan sakamakon matsin lambar hare-haren da sojoji ke kai wa maɓoyarsu.

    A cewar rundunar, mutumin ya miƙa wuya ne jiya ranar 25 ga Yulin 2026 ga dakarun da ke ƙarƙashin Rundunar Task Force ta 24 a kan hanyar Ladari–Jegarawa–Tunokalia da ke kan babban titin Gamboru zuwa Wulgo.

    Binciken farko ya nuna cewa mutumin shi ne babban jami’in kula da kuɗaɗe da kayan aikin sansanin ISWAP da ke Jubillaram.

    Ya miƙa wuya tare da yara maza biyu, yayin da aka ƙwace makamai da sauran kayan ayyukansu.

    Rundunar ta ce miƙa wuyan irin wannan babban jigo na ISWAP wata babbar koma baya ce ga ƙungiyar, domin yana nuna yadda tsarin shugabanci da hanyoyin samar mata da kuɗi ke ci gaba da rushewa.

  5. Wani jirgin dakon mai ya tarwatse a mashigar Hormuz

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa wani jirgin dakon mai ya tarwatse a mashigar ruwa ta Hormuz bayan ya taka nakiyar ruwa, bayan da ake zargin ya kauce daga hanyar da hukumomin Iran suka ware domin zirga-zirgar jiragen ruwa.

    Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ce binciken farko ya nuna jirgin ya fita daga amintacciyar hanyar ruwa duk da gargaɗin da aka yi masa a baya.

    Rahoton ya kuma ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin zirga-zirgar jiragen ruwan ƙasashen waje da kuma wasu jiragen da ake zargin suna karya dokokin zirga-zirga a yankin.

    Har yanzu ba a fitar da ƙarin bayani game da asarar rayuka ko lalacewar da aka samu ba.

    Lamarin na zuwa ne duk da cewa hare-haren da Amurka da Iran ke kai wa juna sun tsaya na tsawon kwanaki biyu, yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da ƙoƙarin dawo da ɓangarorin biyu kan teburin tattaunawa.

  6. Gwamnatin Sokoto ta nesanta kanta da boka 'Mai Shaho'

    Gwamnatin Jihar Sokoto, ta nesanta kanta daga ayyukan wani mai sihiri da aka fi sani da suna Mai Shaho.

    Ta dauki wannan matakin ne biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa na zamani, inda a ciki aka gan shi yana binne bunsuru da rai.

    A cikin bidiyon, mutumin ya binne dabbar ne sannan ya ce ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar ba zai samu nasara .

    A wata sanarwa da Abubakar Bawa, daraktan hulda da jama'a na gidan gwamnatin Sokoto ya fitar, gwamnatin ta ce, ba ta da wata alaƙa da mutumin da ma ayyukansa. Sanarwar ta kara da cewa ko kadan gwamnatin jihar ba ta goyon bayan masu sihiri.

    “Jihar Sokoto jiha ce da galibin al’ummarta Musulmai ne, kuma mutanenta suna riƙe da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa, da kuma bin sawun mujaddadi Sheikh Usman Dan Fodiyo. Don haka, Gwamnatin Jihar ba za ta amince da duk wani aiki ya saɓa wa koyarwar Annabi Muhammad SAW ba.”

  7. Shugaban Senegal ya ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa

    Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna Kiiray (Jam’iyyar Republican Patriots), lamarin da ke nuna ƙara tsananta rabuwar kai tsakaninsa da tsohon abokinsa kuma tsohon fFiraminista, Ousmane Sonko.

    An ƙaddamar da jam’iyyar ne a Dakar tare da halartar ɗaruruwan magoya baya.

    Ƙaddamarwar ta zo ne a lokacin da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Pastef suka koma goyon bayan Shugaba Faye.

    A halin yanzu, Sonko wanda shi ne Kakakin Majalisar Dokokin ƙasar, yana goyon bayan sauye-sauyen kundin tsarin mulki da za su hana shugaban ƙasa jagorantar jam’iyya a lokaci guda.

    Ana sa ran za a gwada ƙarfin siyasar mutanen biyu a zaɓukan ƙananan hukumomi da za a yi a shekarar 2027.

  8. Amurka da Iran sun amince da komawa tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙi

    Amurka da Iran sun mayar da martani ga wata shawarar sasanci da Pakistan da Qatar suka gabatar domin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu, inda rahotanni suka ce ɓangarorin biyu sun amince da amfani da tattaunawa da diflomasiyya domin dakatar da faɗa.

    Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ruwaito cewa shirin ya haɗa da komawa yanayin da ake ciki kafin sabon ɓarkewar yaƙin kwanaki 17 da suka gabata da kuma dawo wa teburin tattaunawa.

    Majiyoyi sun ce an dakatar da hare-haren da Amurka da Iran ke kai wa juna tsawon kwana biyu, bayan wata tawagar diflomasiyyar Oman ta kai ziyara Tehran.

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Amurka sun nuna cewa Donald Trump ya yanke shawarar dakatar da kai haren soja a kan Iran a yanzu, yayin da Iran ta ce ta dakatar da hare-harenta saboda manufarta ta kasance mayar da martani ne kawai.

    Pakistan da Qatar na ci gaba da ƙara yunƙurin sasanci, inda suka bayyana dakatar da hare-haren a matsayin mataki mai ƙarfafa gwiwa wajen neman zaman lafiya.

  9. Gwamnatin Sokoto ta nesanta kanta da boka 'Mai Shaho'

    Gwamnatin Jihar Sokoto, ta nesanta kanta daga ayyukan wani mai sihiri da aka fi sani da suna Mai Shaho.

    Wannan ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa na amfani, inda a ciki aka gan shi bunsuru da rai.

    A cikin bidiyon, mutum ya binne dabbar ne sannan ya ce ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar ba zai samu nasara .

    A wata sanarwa da Abubakar Bawa, daraktan hulda da jama'a na gidan gwamnatin Sokoto, fadar ta ce, ba ta da wata alaƙa da mutumin da ma ayyukansa. Sanarwar ta kara da cewa ko kadan gwamnatin jihar ba ta goyon bayan masu sihiri.

    “Jihar Sokoto jiha ce da galibin al’ummarta Musulmai ne, kuma mutanenta suna riƙe da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa, da kuma bin sawun mujaddadi Sheikh Usman Dan Fodiyo. Don haka, Gwamnatin Jihar ba za ta amince da duk wani aiki ya saɓa wa koyarwar Annabi Muhammad SAW ba.”

  10. Ƴan Ghana 1,000 za su koma gida daga Afirka ta Kudu

    Gwamnatin Ghana ta bayyana cewa ƙarin ƴan ƙasar Ghana 1,000 da ke aiki a matsayin baƙin haure za su fara komawa ƙasarsu ranar Lahadi da Litinin daga Afirka ta Kudu, inda ake ci gaba da zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa tashin hankali kan baƙin haure.

    Tuni hukumomin Ghana suka kwashe ƴan ƙasarta 926 daga Afirka ta Kudu, sannan gwamnatin ta yi kakkausar suka kan waɗannan hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka a babbar tattalin arzikin nahiyar Afirka.

    Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta sanar a daren Asabar cewa jirage na musamman da za su dawo da ma'aikatan baƙin-hauren za su fara isa ƙasar a ranar Lahadi da Litinin. Ta ce wannan shi ne mataki na ƙarshe na shirin kwashe 'yan ƙasar Ghana daga Afirka ta Kudu.

    Shugaban Ghana, John Mahama, ya buƙaci Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanya batun abin da ya kira "hare-haren ƙyamar baki" a Afirka ta Kudu cikin ajandar taronta, yana zargin gwamnatin Pretoria da rashin ɗaukar isassun matakan da za su dakile hare-haren.

  11. 'Ya kamata albashin sojan Najeriya ya kai naira 250,000'

    Manjo Janar John Enenche (mai ritaya) ya yi kira da a ƙara albashin sojojin Najeriya zuwa aƙalla Naira 250,000 a duk wata.

    Manjo Janar John Enenche (mai ritaya) ya yi kira da a sake duba albashin sojojin Najeriya tare da ƙara shi, inda ya ba da shawarar cewa mafi ƙarancin albashin soji ya kamata ya kasance Naira 250,000 a wata.

    Ya ce albashin da ake biya a yanzu bai dace ba duba da halin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya ba.

    Batun ƙarancin albashin sojoji ya sake ɗaukar hankali ne bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa an ƙara mafi ƙarancin albashin sojoji daga Naira 49,000 zuwa Naira 100,000.

    Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ne ta ruwaito shi yana bayyana haka a lokacin da yake magana kan batun albashin sojojin Najeriya a wata hira da ya yi da tashar ARISE TV ranar Lahadi.

    Tsohon daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriyan, ya ce Naira 250,000 da ya ba da shawara a matsayin mafi ƙarancin albashi zai zama mataki na farko mai ma'ana da zai bai wa sojoji damar biyan muhimman buƙatun rayuwarsu na yau da kullum.

  12. Mun dakatar da hare-hare tunda ita ma Amurka ta dakata - Iran

    Kakakin rundunar sojin Iran ya ce Tehran ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a yankin bayan Amurka ta daina kai hare-hare a kwana biyu da suka gabata.

    Kakakin ya jaddada cewa Iran na kallon hare-haren da ta kai a matsayin ramuwar gayya ne kawai.

    Har zuwa yanzu, gwamnatin Amurka ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayyana dalilin dakatar da hare-haren bayan kusan makonni biyu ana kai su.

    Sai dai kafafen yaɗa labarai da dama a Amurka na rahoton cewa Shugaba Donald Trump ne ya yanke shawarar dakatar da hare-haren bayan jami'ai sun nuna damuwa kan raguwar adadin makaman kariya na Patriot da ake da su, tare da fargabar cewa ci gaba da hare-haren na iya janyo rashin jin daɗin ƙawayen Amurka na ƙasashen Larabawa.

    A wani ci gaba kuma, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi da masu shiga tsakani daga ƙasar Oman kan yadda za a tafiyar da zirga-zirga a mashigin Hormuz.

  13. Falasɗinawa sun ce Isra'ilawa ƴan kama-wuri zauna sun ƙona musu masallatai da motoci

    Wasu Yahudawa ƴan kama wuri zauna a Falasdinu sun ƙona masallatai biyu, tare da ƙona motoci da gonakin noma a Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari.

    Haka kuma sun lalata kadarori, tare da yin rubuce-rubuce a bango da fenti, ciki har da kalmar "ramuwar gayya", a wuraren da suka kai harin.

    Sabbin hare-haren sun zo ne kwanaki biyu bayan wani rikici tsakanin Yahudawan ƴa kama wuri-zauna da Falasɗinawa a kusa da ƙauyen Tell, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa huɗu da Isra'ilawa biyu.

    Tun daga lokacin, Falasɗinawa sun ce an kai hare-hare da dama kan ƙauyuka a sassan arewacin Yammacin Kogin Jordan.

    Magajin Garin Qusra ya ce ƴan kama-wuri zauna ɗin sun ƙona wa masallacin da ake ginawa.

    A gefe guda kuma, rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta shirya gidajen wasu Falasdinawa biyu da ake zargi suna da hannu a harbin da ya faru ranar Juma'a domin yiwuwar rusa su.

  14. Me ya sa ake nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Argentina tsana?

    Ko shakka babu kwarewarka a irin wasan da kake bugawa da abokan hamayya kan iya janyo maka ƙaruwar masu fatan ganin faɗuwarka.

    Wani hali da ake ganin ƙasar Argentina da ta ci kofin duniya sau uku ta tsinci kanta ciki.

    Makiya wani lokacin ba dole sai na kusa ba na nesa ma ana tattaro su a zo da su ba tare da lura ba.

  15. Waɗanda suka kamu da Ebola a DR Congo ya haura 3000

    Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ya haura 3,000, yayin da sama da mutum 1,300 suka mutu sakamakon cutar.

    A ranar Asabar, ma'aikatan lafiya da ke aiki a cibiyar kula da masu cutar a yankin Ituri da ke gabashin ƙasar, inda annobar ta fi kamari, sun shiga yajin aiki saboda rashin biyansu alawus na tsawon watanni biyu.

    Kimanin ma'aikata 100 ne suka fice daga aikinsu a birnin Bunia, lamarin da ya kawo cikas ga kula da marasa lafiya.

    Jami'ai sun ce ana kan magance jinkirin biyan kuɗaɗen, kuma ana sa ran za a kammala biyan a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

  16. Brazil ta hana ƴan Amurka masu sa ido kan zaɓe bizar shiga ƙasar

    Wasu rahotanni sun ce Brazil ta ƙi ba wasu jami'an Amurka biyu biza, waɗanda suka shirya zuwa kasar domin duba aka shirya yin zaben kasar wanda za a yi a watan Oktoba.

    Majiyoyin diflomasiyya sun ce jami'an na son nuna shakku kan sahihancin tsarin zaɓen Brazil, zargin da Amurka ta musanta zargin, inda ta bayyana shi a matsayin "ƙarya marar tushe".

    A zaɓen da ke tafe, Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva (Lula) zai fafata da Flavio Bolsonaro, wanda jam'iyyar Liberal mai ra'ayin mazan jiya ta amince da shi a hukumance a matsayin ɗan takararta a ranar Asabar.

    Flavio Bolsonaro na daga cikin abokan siyasar Shugaban Amurka Donald Trump, kuma ya sha bayyana shakkunsa kan amincin tsarin zaɓen da ake yi ta hanyar na'urar kwamfuta a Brazil din.

    Mahaifinsa, tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro, na zaman hukuncin daurin kurkuku bayan an same shi da laifin shirya wani yunkurin juyin mulki, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  17. Ana ci gaba aiki ceto waɗanda gobarar dajin Spain ta rutsa da su

    Firaministan Sifaniya, Pedro Sánchez, ya ce 'yan kwana-kwana na ci gaba da aiki domin ceto rayuka yayin da gobarar daji ke ci gaba da ruruwa a yankunan da ke yammacin birnin Madrid.

    Sánchez ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara yankin da gobarar ta shafa, inda aka umarci sama da mutum 90,000 su fice daga gidajensu ko kuma su zauna a cikin gidajen ba fita saboda matakan kariya.

    A babban birnin kansa, mazauna na sanya safar fuska tare da rufe tagogin gidajensu yayin da hayaƙi da kauri na gobarar ke bazuwa.

    A wani lamari daban, mutum daya ya rasu sakamakon wata gobarar a gabashin ƙasar. Gwamnatin kasar ta Sifaniya ta ayyana dokar ta-baci ta ƙasa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin shawo kan gobarar.

    Ana kuma fatan cewa sauyin yanayi da ake sa ran samu nan gaba kaɗan zai taimaka wa jami'an agaji da na kashe gobara wajen dakile yaɗuwar wutar.

  18. Faransa ta umarci ƙarin mutum 55,000 su fice daga gidajensu saboda gobarar daji

    Hukumomi a kudu maso yammacin Faransa sun umarci karin mutum 55,000 da su fice daga gidajensu a yankunan da ke kusa da birnin Bordeaux, yayin da mummunar gobarar daji ke ci gaba da bazuwa.

    A yanzu, kusan mutum dubu 250 ne aka umarta su bar gidajensu saboda barazanar gobarar. Firaministan Faransa ya yi gargadin cewa yanayin da ba ya da kyau, ciki har da iska mai ƙarfi da tsananin zafi, na ƙara daburta ƙoƙarin da jami'an kashe gobara ke yi na shawo kan lamarin.

    Wakilin BBC ya ce rahotannin da aka bayar da farko ranar Asabar na cewa kila tsananin gobarar dajin da ke ta'annati a Faransa ya ragu.

    A wani mataki na musamman, gwamnatin Faransa ta tura wani katafaren jirgin sama na soji na dakon kaya karo na farko domin watsa sinadaran kashe gobara a yankunan da gobarar ta fi ƙamari a kusa da birnin na Bordeaux.

  19. Ƴansanda na neman matashin da ya kutsa taron masu neman jinsi a Jamus

    'Yan sanda a birnin Berlin na Jamus sun shafe dare suna neman direban wata mota da ta kutsa cikin taron mutane a ɗaya daga cikin manyan tarukan masu neman jinsi daya a Turai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mace daya da jikkata mutum 16.

    Wakilin BBC ya ce 'yansanda na amafani da jirgin sama mai saukar ungulu da fitilu masu haske a neman wanda ake zargin a cikin duhun wannan waje na tsakiyar Berlin.

    Hukumomi sun ce babban wanda ake zargin matashi ne mai shekara 21 mai suna Abdul B, kuma yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi na ikirarin jihadi.

    'Yan sanda sun kuma ce an caka wa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa wuƙa bayan aƙalla mutum ɗaya daga cikin maharan ya fito daga cikin motar kafin ya tsere daga wurin.

    Dubban mutane ne suka halarci taron na shekara-shekara na masu rajin kare haƙƙin masu neman jinsi daya, a babban birnin na Jamus, gangamin da ake wa lakabi da Christopher Street Day.

  20. Trump zai dakatar da yunƙurin faɗaɗa hare-hare a Iran

    Rahotanni da dama daga Amurka sun ce Shugaba Donald Trump ya yanke shawara, a halin yanzu aƙalla, kada ya ƙara faɗaɗa hare-haren sojin Amurka kan Iran.

    Rahotannin sun ce Trump ya ɗauki matakin ne shekaran jiya Juma'a, bayan da wasu jami'ai suka nuna damuwa game da raguwar makamai masu linzami na kariya na Patriot, masu tsada sosai, da kuma yiwuwar matakin ya haifar da saɓani tsakaninsa da ƙawayen Amurka na ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Fasha.

    Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin, sai dai Fadar White House ta ce Trump koyaushe ya fi son a warware matsaloli ta hanyar diflomasiyya.

    Daren Juma'a ne karo na farko cikin kusan mako biyu da ba a kai hare-haren sama na Amurka kan Iran ba. Haka kuma ba a kai irin waɗannan hare-hare ba a daren Asabar.