'Mahaifiyata ta yi min ƙaryar ciwo na shekaru kafin likita ya gano gaskiya'

    • Marubuci, India Rakusen
    • Marubuci, Radek Boschetty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Outlook*
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A lokacin da take tasowa a ƙasar Netherlands a tsakankanin shekarun 1970 zuwa 1980, Nina Blom ta fara rayuwa ne kamar sauran yara.

Ta kasance tana sha'awar waƙoƙi da rawa, kuma takan tuna yadda suke yawan wasa da ƴar uwarta a gida.

Amma duk da haka, ba kasafai take samun lokacin nishaɗi da yara ƴan'uwanta ba. Sannan tana ƴar shekara takwas ne mahaifiyarta ta fara faɗa mata cewa tana fama da rashin lafiya.

Sai ta fara kai ta asibiti domin gwaje-gwaje da jinya, inda ta je har asibiti aƙalla guda 15.

Haka ta sa Nina ta koma zama a kujerar guragu, sannan ta bayyana mana cewa cutar ta tsananta.

An duba ta a asibitoci da dama, amma ba a gano abin da ke damunta ba.

Wani likita guda ɗaya ne ya dage wajen gano gaskiyar lamarin. Asalin matsalarta ita ce: Mahaifiyarta kamar yadda likitan ya gano.

Cutar Paediatric Condition Falsification, wadda ake kira Fabricated or Induced Illness (FII) ko kuma Munchausen Syndrome by Proxy, wata cuta ce da masu kula da marasa lafiya musamman iyaye suke ta'azzara rashin lafiyar ƴaƴansu.

Sai dai har yanzu ba a fahimci asali da haƙiƙanin abin da ke janyo hakan ba.

Zuwanta asibiti na farko

A lokacin da Nina take shekara takwas ne ta fara fama da ciwon ciki, sannan ta rame sosai.

Da aka kai ta asibiti sai aka ba ta wata miya ta sha, sannan ta sha lemun apple, kwatsam sai ta fara samun sauƙi.

"Da an duba ta sai likita ya ce lafiyarta ƙalau, ta koma gida."

Amma sai mahaifiyar Nina ta dage cewa ita fa lallai ƴarta ba ta da lafiya, sai ta koma asibiti, inda ta tilasta yarinyar ta riƙa cewa cikinta na ciwo duk kuwa da cewa ba ta jin komai.

Haka ta cigaba da ziyara zuwa asibitoci daban-daban. Wata rana Nina ta yi ƙorafin cewa tana jin zafi a jikinta, kawai sai mahaifiyarta ta ce dole su koma asibiti domin a cewarta ta kamu da cutar gaɓɓai.

Wata rana Nina ta yi jayayya da mahaifiyar, sai ta ce mata, "kar ki yi jayayya da ni. Ba ki da lafiya, kuma asibiti za ki je."

A wajen Nina, sai lamarin ya ɗaure mata kai.

"Sai hankalina ya tashi saboda na tsinci kaina ne a kwance a asibiti tare da wasu yaran masu cutar cancer waɗanda suke matuƙar rashin lafiya. Amma ni kuma na san cewa lafiyata ƙalau."

Watarana sai wani yaro da ke kwace a kusa da ita ya mutu, lamarin da ya ƙara ɗaga mata hankali.

'Ba ta da tausayi'

An yi wa Nina gwaje-gwaje, ciki har da gwajin ɓargo mai wahala da zafin gaske, amma babu abin da likitocin suka gani.

Duk lokacin da aka kai ta asibiti, sai mahaifiyar ta tsaya a kanta. Da zarar ta ga Nina na murmushi, sai ta fara faɗa.

Wani lokacin sai da ta yi mako huɗu a asibiti, da likitan ya ga babu komai sai ya ce ta koma gida. Suna komawa gida sai mahaifiyar ta tursasa ta fara zama a kujerar guragu, ta cire ta a makaranta, sai ta tilasta mata kwanciya a gado a gida.

Sai ta daina haɗuwa da ƙawayenta, sannan ta hana sauraron waƙoƙi. Da farko ta koma saƙa, amma har hannayenta suka gaji ta daina. Sai mahaifiyar ta ce akwai matsala a hannun ne, sai ta nannaɗe mata hannayen.

Yanayin ɗaurin da aka yi hannayen ya sa suka fara kumbura - wanda kuma alamu tamkar ya faranta ran mahaifiyar.

"Ban san yadda zan iya bayyana irin baƙin cikin ganin tamkar mahaifiyata tana farin ciki idan ina cikin raɗaɗi ba."

'Mutuwa za ki yi'

Daga baya sai mahaifiyar ta canja salo. Ta zaunar da ita ta faɗa mata cewa, "idan har na lura lafiyarki garau, ni zan miki rauni." Lamarin da ya ƙara tayar da hankalin Nina matuƙa.

Saboda daɗewar da ta yi da hannaye a ɗaure, sai jikinta ya ƙara rauni inda aka tura ta asibitin kula da yara da gyara musu tunani.

A asibitin ne ta sake koyon tafiya, sannan ta faɗa soyayya da wani yaro da shi ma mara lafiya ne, sannan ta fara samun nishaɗi da walwala.

Amma da zarar ta koma gida a ƙarshen mako, sai mahaifiyar ta sake tilasta mata komawa tamkar mara lafiya tare da tursasa ta kwanciya a gado.

Watarana sai mahaifiyar ta faɗa mata cewa ta kamu da cutar zuciya, "mutuwa kawai za ki yi."

"Wannan lokacin ne na faɗa damuwa mafi girma," in ji Nina.

'Likita ina so ta mutu'

Daga nan sai abubuwa suka fara canjawa, bayan Nina ta haɗu da wani likitan yara mai suna Dr Vrienten.

Sai ya ce mata zai samu wani waje da ƙwararru za su taimaka wajen inganta gaɓɓai da hannayenta domin ta koma tafiya da kyau.

Sai abin ya ba Nina mamaki saboda mahaifiyarta ta sha bayyana mata cewa gaɓɓan sun mutu kuma ita ma mutuwa za ta yi. Tun da farko dai tana shakka, amma ba ta taɓa tambaya ba.

Da mahaifiyar ta ji haka, sai ranta ya ɓaci. Ta nannaɗe ƙafar Nina, ta sanya matashiyar kai a tsakani. Ta taƙaita mata abinci, sannan ta saka mata bututun cin abinci ta hanci, sannan ta riƙa ba ta magani ƙwaya 20 a kullum.

Watarana da likitan ya duba Nina, sai ta ce yarinyar ta jigata da yawa, "likita ina so kawai ta mutu. Za ka iya taimaka mana ta mutu?"

Likitan sai ya koma baya, ya faɗa mata wani abu, sannan ya rubuta wasu maganin morphine. "Za mu sa ta fara barci," in ji shi.

Aikin ceto

Amma a lokacin Dr Vrienten ya riga ya kira sashen kula da yara domin su kawo agajin gaggawa.

Watarana kawai sai wata mata ta shiga ɗakin da Nina ke kwance ta faɗa mata cewa za ta kai ta wani asibitin daban.

Sai Nina ta fara roƙonta, "don Allah ki bari kawai in mutu."

Sai ta lura mahaifiyarta ta fara ruɗewa, kuma ƴansanda guda biyu sun shigo ɗakin suna tsaye.

Sai aka ɗauke ta ka sata a motar asibiti aka tafi da ita zuwa asibiti sannan aka saka na'urar naɗar bidiyo a ɗakin.

Amma kwana biyu da kai ta asibitin iyayenta babu wanda ya zo duba ta. Daga baya da suka je, sai Nina ta faɗa musu cewa, "ni lafiyata ƙalau, babu abin da ke damuna."

Sai da ta maimaita cewa lafiyarta ƙalau sau 18.

Mahaifiyar wadda ta manta cewa bidiyo na naɗar komai ta fusata ta fara bayyana abin da ya riƙa faruwa a baya.

Sabuwar rayuwa

Baya wani lokaci, sai Nina ta yanke alaƙa da iyayenta baki ɗaya. Bayan ta yi jinya ta gama, sai ta koma wani garin da suna daban.

A can ta fara sabuwar rayuwa, inda ta kammala karatu ta samu aiki, har ta fara soyayya.

Iyayenta ba su taɓa aminta da abin da suka yi ba, wani lokacin ma har ɗaukar mai bincike na musamman suka yi domin ya nemo ta, lamarin da ya sake jefa ta cikin wata damuwa.

Sai ta fara tunanin kai su ƙara, kasancewar bayan an ceto ta, babu wanda ya kai ƙararsu, amma sai ta fasa kai ƙarar. Daga ƙarshe dai iyayen duka sun rasu ɗaya bayan ɗaya.

"Abin da iyayenmu suka aikata laifi ne. Cin zarafin yara ne, kum da ƙyar na sha," in ji ta.

Amma kuma tana farin cikin kasancewar ta fara sabuwar rayuwa.

"Ina farin cikin tsira da na yi, kuma rayuwa tana da faɗi."