BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Abin da ke ƙunshe a cikin wasiƙar da Trump ya rubuta wa Tinubu
Wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira "ƙwazon jagorancinsa" wajen yaƙi da ta'addanci da kuma magance matsalar tsaro a Najeriya.
KAI TSAYE, Trump ya sanar da ƙara haraji ga ƙasashe ciki har da Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 24/07/2026
Madrid za ta saurari tayin Utd kan Tchouaméni, Arsenal na neman Stones
Real Madrid za ta saurari tayin sayen ɗan wasanta, Aurélien Tchouaméni, na Faransa, daga Manchester United, yayin da Arsenal ke son Stones da Konsa.
Abubuwan da suka sauya a Nijar shekara uku bayan juyin mulki
Nijar ta yi fama da juyin mulkin sojoji har sau huɗu tun bayan samun ƴancin kai daga Faransa a 1960.
Abin da BBC ta gani a makarantar da aka kashe ɗalibai 120 a Iran
Manyan ɓuraguzan siminti suna reto daga saman benen da ya lalace. Har yanzu akwai wasu azuzuwa da ba su lalace ba tare da bangon da aka yi wa ado da zanen balan-balai da furanni masu launuka.
Abubuwan da yarjejeniyar nukiliyar Amurka da Saudiyya ta ƙunsa
Amurka da Saudiyya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da za ta bai wa masarautar Saudiyya damar bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya.
Iran ta gargaɗi Birtaniya bayan harin jirgin B-1
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 23 ga watan Yuli, 2026.
Kotu ta yanke wa waɗanda suka sace ɗaliban Oyo hukunci
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa wasu mutane uku hukuncin ɗaurin rai da rai da aka kama bisa hannu a garkuwa da ɗaliban jihar Oyo da malamansu a karamar hukumar Oriire.
Wane ne Abu Salim al-Barnawi, mai ɗaukar hoton ISWAP da sojojin Najeriya suka kashe?
Asali yana cikin mayaƙa ne masu kai hare-hare, kafin daga bisani aka mayar da shi ɓangaren ɗaukar hoto da yaɗa ayyukan ƙungiyar.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Rana, 13:59, 24 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 24 Yuli 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 24 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 23 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Guardiola na dab da zama kocin Italy
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran Gasar Kofin Duniya da aka kammala da kuma sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 20 zuwa 26 ga watan Yuli, 2026.
Tottenham na sa rai kan Savinho, Madrid ta ja da baya kan Rodri
Tottenham na da kwarin gwiwar sayen Savinho daga Manchester City, ita kuwa Real Madrid ta fara hakura da maganar Rodri, yayin da AC Milan ke sa ido a kan Phil Foden.
Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Afirka ta mata ta 2026
An bayyana dalilan da suka sa aka jinkirta gasar, wadda ya kamata a fara a watan Junin da ya gabata.
Ƴanwasa 5 da suka samu manyan kyautuka a Gasar Kofin Duniya
A kowace Gasar Kofin Duniya da FIFA ke shiryawa takan lura da wasu ƴanwasan da suka fi fice a fannoni daban-daban domin karrama su kan rawan da suka taka a gasar.
Chelsea, Arsenal da Spurs na zawarcin Rashford, Arsenal na son Konsa
MAnyan ƙungiyoyin Firimiya na zawarcin Marcus Rashford, yayin da Arsenal ke harin ɗan wasan Aston Villa Ezri Konsa, sai Nottingham Forest da ke neman sabon ɗan wasan baya.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ake yi da kadarorin da ake ƙwacewa daga waɗanda ake zargi da sata a Najeriya?
Majalisar Wakilan Najeriya ta bijiro da binciken yadda ake gudanar da kadarorin da gwamnati ke ƙwacewa daga hannun mutanen da ake zargi da rashawa a ƙasar.
Da gaske gajimare ne ya faɗo a hanyar Abuja zuwa Kaduna?
Tun a makon da ya gabata ne abun ya fara ɗaukar hankalin matafiya, waɗanda suke sauka daga ababen hawansu tare da shiga cikinsa domin ɗaukar hotuna.
Me ya sa wasu ƙasashen Afirka ke ƙin karɓar kuɗaɗen tallafin Trump?
Bayan rusa babbar hukumar Amurka da ke bayar da tallafin ƙasashen waje a bara, gwamnatin Trump na sake bayar da ɗaruruwan miliyoyin daloli ga ƙasashen Afirka, domin tallafa wa tsarin kiwon lafiyarsu da kuma yaƙi da cututtuka.
Ko barazanar Houthi ta rufe Bab al-Mandab ka iya haddasa sabon rikicin jigila a tekun Maliya?
Mashigin mai tsawon kusan kilomita 115 da faɗin kilomita 36 na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin kasuwanci a duniya tun bayan buɗe Mashigin Suez a shekarar 1869, wadda ita ce mafi gajartar hanyar ruwa tsakanin Turai da Asia.
Wane hali ake ciki kan ceto ɗaliban da aka sace a Borno?
Fiye da wata biyu bayan sace ɗalibai a makarantu uku da ke garin Mussa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu iyaye na jiran ganin an ceto ƴaƴan nasu.
Ma'aikatun Najeriya 5 da suka fi yawan ma'aikatan bogi - ICPC
Shugaban hukumar Barsita Musa Aliyu SAN, ya tabbatar wa BBC an gano ma'aikatan bogin ne bayan wani bincike da hukumarsa ta ƙaddamar a 2024.
Yadda tsawa ta kashe yara 6 ƴan gida ɗaya a Adamawa
"Abin da ya faru da ruwan sama ya fara sauka sai wata mata wadda take da ƙaramin yaro ta buɗe lema a kusa da wata bishiya. Su kuma yaran duk sai suka taru a ƙarƙashin lemar. To da tsawar ta faɗo shi ne ta yi musu haka," in mai unguwa.
Wane ne Khalil al-Hayya, sabon shugaban ƙungiyar Hamas?
Al-Hayya, wanda a baya ya kasance jagoran ƙungiyar Hamas a ƙasashen waje, ana kallonsa cikin masu tsattsauran ra'ayi a Hamas, wanda ya fito fili a lokacin yaƙin Isra'ila da Hamas da ya fara kusan shekaru uku da suka gabata.
Masu horaswa 6 da suka rasa aikinsu bayan gasar Kofin Duniya
Wasu ƙasashe kuwa irinsu Tunisia tun a wasan farko na gasar suka sallami mai horaswa saboda gaza yin abin da aka yi tsammani
Me ke janyo yawan kifewar kwale-kwale da ke kisan ƴan Najeriya?
Kifewar kwale-kwale na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo asarar rayuka a Najeriya, musamman a yankunan da ake amfani da koguna ke a matsayin hanyar sufuri ta yau da kullum.
Yadda cacar baki ta kaure tsakanin APC da Kwankwaso akan matsalar tsaro
Jam’iyyar APC ta mayar da zazzafan martani akan kalaman Kwankwaso da ya bayyana gazawarta a ɓangaren tsaro
Ko Iran za ta cigaba da jure wa rashin ganin jagoranta Mojtaba Khamenei?
Fiye da wata huɗu bayan maye gurbin mahaifinsa a matsayin sabon jagoran addinin Jamhuriyar Musulumci ta Iran, har yanzu ba a ga sabon jagoran ba.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































