Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rundunonin sojin Najeriya 12 da jihohin da suke karewa
Tsawon lokacin da aka ɗauka ana fama da ƙalubalen tsaro a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar ya sanya ake yawaitar kiraye-kirayen gwamnati ta sauya salo da kuma matakan da take ɗauka a kan batun.
Daga cikin kiraye-kirayen da aka daɗe ana yi har da cewa gwamnatin ta ƙara yawan jami'an tsaron ƙasar, musamman sojoji waɗanda su ne kan gaba a yaƙi da matsalar tsaron kuma da dama ana ganin cewa sun yi ƙaranci ta la'akari da yadda matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Duk da cewa a baya an ga yadda gwamnatoci suka yi wani abu mai kama da amsa waɗannan kiraye-kiraye, ta hanyar sanar da shirin ɗaukar ƙarin dakarun soji a Najeriya, shugaban Bola Tinubu ya sanar da faɗaɗa rundunonin sojin da ke aiki a faɗin ƙasar daga 8 zuwa 12.
Gwamnatin Tinubu ta ce ta ɗauki mtakin ne da nufin ƙarfafa tsarin tsaro da inganta ayyukan sojin Najeriya.
Me masana tsaro ke cewa?
Masana tsaro a Najeriya irin su Group Captain Sadiq Shehu mai ritaya na ganin cewa duk da dai babu jayayya kan buƙatar ƙara yawan dakarun tsaron Najeriya, akwai hanyoyin da suka fi dacewa a bi domin samun nasara.
Tsohon jami'in sojin ya ce dama masana sun daɗe suna kira kan Najeriya ta gaggauta ƙara yawan dakarunta, saboda girman matsalar tsaro da take fama da ita da kuma tasirin ta a tsakanin ƙasashen Afirka.
Ya ce zancen ƙarancin jami'an tsaro a Najeriya wani abu ne a bayyane, ''idan muka duba alƙalumma duk da dai sojoji ba su cika son a faɗa ba, amma lokacin marigayi shugaban ƙasa Buhari lokacin da ministan tsaro ya ce 'da sojin ruwa da na sama da kuma na ƙasa, a lokacin Najeriya tana da 230,000'.''
Group Captain Sadiq Shehu ya ƙara da cewa ''a lokacin muna da 'division-division' (rundunoni) takwas, amma yanzu ana so a kai su 12.
To 'division' a aikin soja yadda aka yi koyi da Amurka da Ingila, ana neman soja aƙalla 10,000 zuwa 20,000 da suka haɗa da hafsoshi da ƙananan jami'ai domin kafa runduna guda. Ba a zo kan maganar kayan aikin su ba.''
Masanin tsaron ya ce a yadda yake kallon batun, hatta rundunoni takwas da Najeriya ke da su a ƙasa ba su da cikakkun kayan aiki, don haka ba su kai yadda ake zaton su a takarda ba.
''Duk da an yarda cewa babu isassun sojojio, ina ganin abin da ya kamata a yi shi ne a cika waɗannan rundunonin da yanzu ake da su, saboda idan aka ce za a ƙara wasu 12 bayan takwas ɗin ma ba su cika ba to zai zamo an yi abin da aka cewa tana da faɗi amma ba ta da zurfi kenan,'' in ji Group Captain Sadiq.
Yadda sabon tsarin zai kasance
Shugaban ƙasar ya amince da ɗaukar ƙarin jami'an soji 28,000, tare da sayen muhimman kayan yaƙi da inganta jin daɗin sojoji da kuma sabunta kayan aikin rundunar.
Gwamnatin ta ce za a kafa sabbin rundunonin ne a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin.
A ƙarƙashin sabon tsarin, rundunar sojin Najeriya za ta kasance da rundunoni 12 da za a kasa su a sassa daban-daban na ƙasar kamar haka:
Runduna ta 1 – Kaduna (Za ta kula da Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa)
Runduna ta 2 – Ibadan (Za ta kula da Oyo, Osun, Ekiti da Ondo)
Runduna ta 3 – Jos (Za ta kula da Filato, Bauchi da Gombe)
Runduna ta 5 – Makurdi (sabuwar runduna - Za ta kula da Benue, Nasarawa da Kogi)
Runduna ta 6 – Fatakwal (Za ta kula da Rivers, Akwa Ibom da Cross River)
Runduna ta 7 – Maiduguri (Za ta kula da Borno da Yobe)
Runduna ta 8 – Sokoto (Za ta kula da Sokoto, Kebbi da Zamfara)
Runduna ta 9 – Ilorin (sabuwar runduna - Za ta kula da Kwara da Neja)
Runduna ta 10 – Jalingo (sabuwar runduna - Za ta kula da Taraba da Adamawa)
Runduna ta 81 – Legas (Za ta kula da Legas da Ogun)
Runduna ta 82 – Enugu (Za ta kula da Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi da Imo)
Runduna ta 83 – Benin City (sabuwar runduna - Za ta kula da Edo, Delta da Bayelsa)
Gwamanatin ta ce za a aiwatar da wannan sauyi ne ta matakai biyu.
Mataki na farko, wanda ya ƙunshi kafa rundunoni na 5, 9 da 10 tare da sake tsara wasu rundunonin da ake da su, inda ake sa ran kammala shi zuwa Satumba 2026.
Mataki na biyu, zai kafa runduna ta 83 da ƙarin gyare-gyare a tsarin rundunar, kuma za a kammala shi zuwa Disamba 2026.