MDD ta buƙaci a kuɓutar da matuƙa jiragen ruwan da suka maƙale a Hormuz
Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira ga ƙasashen da ke da hannu a yaƙin Iran su taimaka wajen fitar da matuƙan jiragen ruwa kusan 6,000 da suka maƙale a mashigar Hormuz.
kakakinsa ya ce ya kamata ɓangarorin da ke rikicin su sauƙaƙa hanyoyin da za su ba su damar wucewa cikin aminci.
Yayin da faɗan ke ci gaba da tsananta, hukumomin Iran sun gargaɗi fararen hula su nisanci sojojin Amurka da ke yankin.
Haka kuma Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kadarori da sansanoni Amurka, a matsayin martani ga hare-haren bama-bamai da Amurka ke ci gaba da kai mata.