Wane ne asalin wanda ya kafa jam'iyyar ADC?

Shugabanni

Asalin hoton, Nafi'u/Mark/Facebook/https://adc.org.ng

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin da fitattun ƴan siyasa suka fara komawa jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a shekarar 2025 domin kafa haɗakar adawa gabanin zaɓen 2027, mutane da dama sun yi ta tambayar kansu: Wace irin jam'iyya ce ADC? Ta yaya ta kai matsayin da take a yau?

Tsawon kusan shekara 20 ke nan ADC ta wanzu, kuma ta kasance cikin jam'iyyun siyasa da Hukumar INEC ta san da zamansu sannan ta fafata a zabuƙan ƙasar a zaɓukan da suka gabata.

Sai dai duk da kasancewarta cikin fafatawar siyasa, ba ta taɓa samun irin karɓuwar da manyan jam'iyyun APC da PDP suka samu ba.

Amma zuwan sabuwar haɗakar adawa ya sauya mata yanayi, inda ta zama ɗaya daga cikin jam'iyyun da ake yawan magana a kansu, har wasu ke mata kallon babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar.

Sai dai rigingimu sun mata dabaibayi, inda ƴaƴanta suke ta fama da shari'o'i daban-daban a kotuna daban-daban na ƙasar, musamman kan shugabancinta da kuma ƴan takararta.

Amma shin su wane ne suka kafa jam'iyyar, kuma wace rawa ta taka a zaɓukan baya, kuma su wane ne suka riƙe ta zuwa yanzu?

Sauya suna

An kafa jam'iyyar ne a shekarar 2005 da sunan Alliance for Democratic Change a farko, kamar yadda shafinta na intanet ya nuna.

Amma daga baya ta sauya suna zuwa African Democratic Congress (ADC), wanda ta ce ta yi ne a lokacin domin nuna faɗaɗa manufofinta da hangen nesan da ta yi a siyasa.

A shekarar 2006, Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta yi wa jam'iyyar rajista a hukumance, lamarin da ya ba ta damar fara shiga manyan zaɓukan Najeriya a dama da ita.

Tun daga kafuwarta har zuwa shekarar 2025, Ralph Nwosu ne ya kasance shugaban jam'iyyar na ƙasa kuma jagoranta.

Sai dai yayin shirin kafa jam'iyyar haɗakar adawa, ya sauka daga muƙaminsa, inda tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya karɓi ragamar shugabancin jam'iyyar.

Ralph

Asalin hoton, https://adc.org.ng/leadership

Shiga zaɓuka

Jam'iyyar ADC ta fara shiga babban zaɓen ƙasa a shekarar 2007, inda ta tsayar da ƴan takara a kujeru daban-daban, ciki har da farfesa Patrick Utomi, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Ko da yake ya samu ƙuri'u 50,849 ne kacal, wanda ya sa ya zo na huɗu, zaɓen ne ya buɗe wa ADC ƙofar shiga dukkan zaɓukan shugaban ƙasa da aka gudanar tun daga lokacin.

Daga 2007, waɗanda suka tsaya takarar shugaba ƙasa a jam'iyyar su ne:

  • Patrick Utomi (2007)
  • Rev. Peter Uchenna Nwangwu (2011)
  • Dr. Mani Ibrahim Ahmad (2015)
  • Obadiah Mailafia (2019)
  • Dumebi Kachikwu (2023)

Samun gurbi a Majalisar Tarayya

Zaɓen shekarar 2011 ne ya kasance muhimmiyar shekara ga jam'iyyar, bayan da ta samu wakilci a majalisar tarayya.

A zaɓen 2015, jam'iyyar ta ƙara ƙarfafa matsayinta, inda ta lashe kujera biyar a majalisar wakilai, duk daga Jihar Oyo. Wannan ya ƙara nuna cewa ADC na ƙoƙarin kafa kanta a matsayin wata jam'iyya mai ƙarfi.

A zaɓukan 2015 da na 2019, jam'iyyar ta fi mayar da hankali kan inganta shugabanci nagari, bai wa matasa dama, da kuma jawo ƙwararru cikin harkokin siyasa.

Wani babban sauyi ya zo ne a shekarar 2018, lokacin da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da ƙungiyarsa ta Coalition for Nigeria Movement (CNM) za ta yi aiki da ita.

Obasanjo ya bayyana cewa manufar hakan ita ce haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo sauyi mai amfani ga siyasa da shugabancin Najeriya.

Sai dai duk da wannan goyon baya, jam'iyyar ba ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2019 ba.

Ce-ce-ku-ce a zaɓen fidda gwani na 2023

Shirin jam'iyyar na shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya gamu da matsaloli da dama daga cikin gida.

An samu saɓani tsakanin fitattun masu neman takara, ciki har da tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Kingsley Moghalu, da kuma Dumebi Kachikwu.

Daga ƙarshe, Kachikwu ne ya zama ɗan takarar jam'iyyar bayan zaɓen fidda-gwanin da ta yi. Sannan da aka gudanar da babban zaɓen na ƙasa, sai ya samu ƙuri'u 78,930 kacal.

Rikicin cikin gida

Kamar yadda ake samu a wasu jam'iyyun siyasar Najeriya, ADC ma ta fuskanci rikicin shugabanci.

A shekarar 2022, Mai shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige Ralph Nwosu daga shugabancin jam'iyyar, tare da ayyana Patricia Akwashiki a matsayin halastacciyar shugabar jam'iyyar.

Kotun ta kuma hana Nwosu da kwamitinsa ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC.

Ko da yake Nwosu ya ɗaukaka ƙara, har yanzu akwai muhawara kan matsayin shugabancin jam'iyyar.

Bayan kafa sabuwar haɗakar adawa a shekarar 2025, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu, ya ce Ralph Nwosu ba shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar ba, yana mai barazanar zuwa kotu kan abin da ya kira ƙwace jam'iyyar da wasu tsofaffin ƴan siyasa suka yi.

Masana siyasa na ganin irin wannan rikici na cikin gida na iya zama ƙalubale ga haɗakar adawar.

Sabon babi

A shekarar 2025, ADC ta shiga wani sabon mataki bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP ya shiga haɗakar adawa da aka kafa a ƙarƙashin jam'iyyar.

Haka kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya shiga haɗakar, sannan Rabiu Musa Kwankwanso da Nasir El-Rufai da sauran jig-jigan ƴan siyasa suka shiga domin haɗuwa su fuskanci APC a babban zaɓen hsekarar 2027.

Shugabannin haɗakar sun ce manufarsu ita ce haɗa kan jam'iyyun adawa domin samar da gagarumar hamayya ga APC a zaɓen 2027, tare da hana Najeriya komawa tsarin jam'iyya ɗaya.

Sai dai ba ta daɗe da shiga haɗakar ba wasu jiga-jigan irin su Peter Obi da Kwankwanso suka fice domin komawa NDC su yi takara, lamarin da ya ɗan cikas ga haɗakar.

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027, tambayar da ake yi ita ce ko ADC za ta iya amfani da wannan sabon haɗakar adawa wajen samun gagarumar nasara a zaɓen?