Me ya sa Iran ta dage kan iko da mashigar Hormuz?

Zanen tsohon jgoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, wana ɗansa Mojtaba ya gada

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Zanen tsohon jgoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, wana ɗansa Mojtaba ya gada
    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Bayan kwana 10 ana musayar luguden wuta tsakanin Amurka da Isra'ila game da iko kan mashigar Hormuz, yanzu dai alamu sun nuna cewa Iran na da zaɓi guda uku ne, amma babu zaɓin buɗe hanyar baki ɗaya.

Zaɓi na farko shi ne ƙasar ta amince da mafi yawan abin da Amurka ke buƙata: Tabbacin wucewa ta mashigar ta hanyar daina kai hare-hare kan jiragen kasuwancin man fetur, dakatar da shirin makamin nukiliya tare da bayar da dama hukumomin sa ida kan makamin su ziyarta cibiyoyin makamin ƙasar.

Ita kuma Iran za ta buƙaci sojojin Amurka ta ɗage takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar, ta samu tabbacin daina hare-hare sannan Amurka ta buɗe filayen jiragen ruwanta da ta buɗe.

Za a iya cewa wannan shi ne mafi sauƙi a ciki, amma kuma a siyasance abu ne mai girman gaske.

Sake buɗe mashigar Hormuz ba tare da tabbacin rawar Iran wajen kula da ita ba, tamkar miƙa abin da wasu ƴan ƙasar suke gani babbar kadarar ƙasar a yaƙi ce, wadda suke ganin ya fi aiki sama da makaman ƙasar masu linzami da ƙungiyoyin da take ɗaukar nauyi da ma shirin nukiliya.

A karon farko, Iran ta nuna ƙwanji wajen nuna ƙarfin ikonta kan tattalin arzikin duniya idan an kai mata hari a ƙasarta.

Shirin makamin nukiliya dai an sha nanata cewa haƙƙin Iran ne da ba zai yiwu a tilasta mata ta watsar ba.

Zaɓi na biyu shi ne a cigaba da gwabzawa. Iran za ta iya cigaba da kai hare-hare a sansanonin sojin Amurka da ke yankin da jiragen ruwa da sauran muhimman wurare a ƙasashen Gulf, inda take tunanin tsadar farashin makamashi zai sa Amurka ta ɗaga ƙafa.

Wannan ne zai fi zafi a sha'anin harkokin soji. Cigaba da ragargazar ƙasashen Gulf zai ƙara kusantar da ƙasashen da shiga cikin yaƙin.

Zaɓi na uku shi ne a cigaba da yadda ake a yanzu: Matsin lamba kan sufurin jiragen ruwa da tsadar makamashi zai sa t cigaba da ja ƙafa, wada bai kai a koma yaƙi gadan-gadan da Amurka ba.

Wannan ya ɗan yi kusa da tunanin ƙasar. Iran ba ta damu da yaƙar ƙasar da take a maƙiyarta ba matuƙar ta yi amannar za ta cigaba da harkokin har na kimanin lokacin da abokiyar karawar za ta iya jurewa da yaƙi. Ita kanta wanzuwar ma nasara ce. Amma takunkumi da yaƙi da asara da tsadar rayuwa duk suna ƙara jawo matsin lamba a cikin ƙasa.

Sai dai kuma wani hanzarin shi ne idan Iran ta cigaba da amfani da mashigar Hormuz a matsayin makamin yaƙi, nan gaba kaɗan za ta iya rage ƙarfi saboda ƙasashe za su fara lalubo wasu hanyoyin kasuwancin makamashi da sauran kayayyaki daban.

Wane ne ke ɗaukar mataki a Iran?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata matsalar ita ce rashin tabbas kan haƙiƙanin wanda ke riƙe da madafun ikon ɗaukar mataki a ƙasar.

A zamanin Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe sakamakon hare-haren Isra'ila da Amurka a Iran a watan Fabrailu, a zarar an samu matsala, shi kawai ake jira ya faɗa yadda za a yi.

Watani bayan kashi shi, har yanzu ana ganin alamu giɓi a shugabancin, musamman wajen ɗaukar mataki.

Shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian da jami'an diflomasiyyarsa za su fi sha'awar sulhunt tsakani domin ɗage takunkumai da samar da zaman lafiya.

Masu tsatsauran ra'ayi a majalisar ƙasar da wasu masu faɗa a ji a ƙasar, ciki har da kafafen watsa labarai suna fargabar muƙa wuya na iya zama matsala kan asalin abin da aka assasa Jamhuriyar Musuluncin ƙasar a kai.

Babban abin da ke jan hankali shi ne batun dakarun juyin-juya-hali. Shirin makamin nukiliya da tsare-tsaren ƙasar kan makomar mashigar hormuz duk suna da alaƙa da matsayar dakarun.

Yanzu babbar matsalar ba wai zaɓin da Iran za ta ɗauka ba ce, matsalar ita ce wanda zai ɗauki mataki kan matsayar ƙasar.

Me Iraniyawa ke cewa?

Iran da Amurka sun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yuni domin kawo ƙarshen yaƙi da buɗe mashigar Hormuz na tsawon kwana 60. Amma kimanin mako uku baya yarjejeniyar, sai shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar ta rushe.

Wata mata a Iran ta shaida wa BBC cewa "ranta ya ɓaci matuƙa" bayan da aka koma yaƙin.

Ta yi tsammanin cewa yarjejeniyar da aka shiga ɗin za ta taimaka wajen fahimtar juna game da sauran buƙatun tare da haifar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Taa zargi masu tsattsauran ra'ayi a cikin gwamnatin Iran da ƙaƙaba wasu matakai masu zafi da ta ce suna illa ga ƙasar.

Ita ma wata mata a Tehran ta ce kamfanonin ƙasashen waje da dama sun kulle, ciki har da wanda take aiki, wanda hakan ya sa ta rasa aikin yi n tsawon wata huɗu duk da cewa tana da digirin digirgir na ƙwarewar shekara 17.

"Ba a ɗaukar aiki a yanzu saboda fargabar abin da zai faru," in ji ta, sannan ta ƙara da tsadar kayayyaki da rashin lantarki da ƙaruwar laifuffuka irin su sace-sace sun shafi harkokin ƙasar.

Shi ma Trump na fuskantar nasa zaɓukan: Ko dai a cigaba da yaƙi ko cigaba da ƙaƙaba takunkumi ko ya amince da amince da wasu buƙatun Iran, musamman Iran ta cigaba da shirin makamin nukiliya a ƙarƙashin kula da sa ido. Sai dai dukkan waɗannan matakan babu wanda yake nufin nasara ga Amurka.