Yadda budurwa ta yanke mazakutar saurayinta a Kano

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Abin mamaki ba ya ƙarewa, inda wata matashiya mai shekaru 25 ta yanke mazakutar saurayinta mai shekaru 25 gabaɗaya a yayin da yake bacci a dakin otal da suka kama a Kano.

Al'amarin dai wanda ƴansandan jihar Kano suka ce ya faru ne a unguwar Badawa a birnin na Kano amma masoyan biyu ƴan jihar Jigawa ne da suka kama otal ɗin.

Kakakin rundunar ƴansanda jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce duk da sun sha samun irin wannan laifi amma wannan ne karon farko da wata ta taɓa yanke gaban namiji baki ɗaya.

Abin da ya faru

Kakakin ƴansandan na jihar Kano, Haruna Kiyawa ya ce al'amarin ya faru a wani otal da ke unguwar Badawa da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin bayan samun rahoto a ranar Litinin ɗin nan.

"Budurwa da saurayi ne inda ita budurwar ta taho tun daga Maigatari na jihar Jigawa ta zo ta same shi a otal a Kano. Kuma tun daga can Jigawa ne ta ɗauko wuƙar da ta yanke masa mazakutar.

Ta yi mana bayani ne cewa lokacin da ta aikata aika-aikar yana bacci kuma adaidai lokacin akwai abin da ya sha da ya sa shi bacci wanda hakan ya ba ta dama ta yanke. Kuma daga nan ta ja shi zuwa banɗaki ta wanke masa jini wanda kuma daga nan ne jama'a suka fahimci akwai abin da ke faruwa," in ji Kiyawa.

Dangane da zargin cewa akwai akwai batun shaye-shaye, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa BBC cewa yanzu bincike dangane da wani lemon Lacasera da jami'ansu suka samu a ɗakin.

"Ita dai daga bayanin da ta yi mana da kuma shaidun da muka samu babu batun maye. Daman ta fada mana cewa ya faɗa mata cewa kansa na ciwo wanda shi ne suka samo maganin ciwon kai ya sha. Kuma akwai Lacasera da ruwa kuma ana bincike a kansu," in ji Kiyawa.

Ko saurayin yana raye?

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa BBC cewa saurayin na da rai kuma yana asibiti yana karɓar magani.

"...yadda ta yanke masa gaban nasa ko guntu ba ta bari ba gaskiya abu ne da ba mu taɓa samun irin wannan kai tsaye ba. Rashin imanin ya yi yawa."

Dangane kuma da a wane halin ita budurwar take, CSP Kiyawa ya ce "yanzu tana hannunmu kuma muna bincike da zarar mun kammala za mu gurfanar da ita a gaban kuliya.