Yadda ƴanbindiga suka bi gida-gida suna 'kashe mutane' a Kauru

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Dama yankin Kauru ba baƙo ne ga hare-haren ƴan bindiga ba, amma wannan shi ne na baya-baya cikin waɗanda aka kai a bayan nan, kuma mafi muni.

Bayanai sun ce ƴan bindiga ne waɗanda yawansu ya kai kimanin da 50 suka afka wa ƙauyen Chawai da ke ƙaramar hukumar Kajuru, suka kashe mutane tare da raunata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi, inda mazauna yankin suka tabbatar da cewa aƙalla mutum 30 ne suka mutu a ƙauyen, kuma wadanda harin ya rutsa da su sun hada da mata da mata, maza da kuma ƙananan yara.

Mutane biyu da BBC ta tattauna da su, Mark Bissan da kuma tsohon kakakin ƙungiyar ci gaban al'ummar Chawai, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai hukumomi a jihar ta Kaduna ba su ce komai ba game da batun.

Ko a watan Janairun wannan shekara wasu mahara sun je ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna, inda suka sace mutane aƙalla 160.

Lamarin ya haifar da ruɗani bayan rundunar ƴansanda a jihar ta musanta faruwar lamarin, amma daga baya ta sanar da cewa ya faru.

Abin da ya faru a cikin dare

Mark Bissan wanda ke a ƙauyen da ke maƙwaftaka, kuma malamin addinin Kirista da ke wa'azi a yankin ya ce: "Mutane na kwance da kimanin ƙarfe 12 sai ƴan bindiga suka shiga, suka fara harbe-harbe suna bi gida-gida suna kashe mutane.

"Mun samu gawa 30, guda 28 ne muka ajiye a mutuware" yayin da bayanai suka ce an yi wa sauran mutum biyu ɗin jana'iza.

Ya bayyana cewa an kashe mata da maza da yara, kuma "yara sun fi yawa".

Duk da cewa yankin kudancin Kaduna ya yi ƙaurin suna kan rikicin manoma da makiyaya, amma Bisan ya ce babu wata rashin jituwa tsakanin al'ummar garin da makiyaya.

Malamin addinin ya ce ƴan bindigan ba su tafi da kowa ba, amma ya ce akwai mutane bakwai waɗanda suke asibiti sanadiyyar harbin bindiga.

Kakakin ƙungiyar ci gaban ƙauyen na Chawai ya ce a halin yanzu al'ummar yankin na cikin barazana, "wata ɗaya kenan da ya wuce muka binne mutum bakwai," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Sai dai mazauna yankin sun koka kan rashin kai ɗaukin jami'an tsaro cikin lokaci, wannan ya sanya matasan garin sun yi wa sojoji bore a lokacin da suka je ƙauyen a washegari.

Hotunan da mazauna yankin suka tura wa BBC sun nuna gidaje da ababen hawa a ƙone yayin da a wasu kuma ake iya ganin gawarwaki waɗanda aka lulluɓe da ganye shimfiɗe a ƙasa.

Sai kuma wasu hotunan da ke nuna lokacin da ake yi wa gawarwakin jana'iza.

Hotunan sun nuna manya da yara kwance a cikin akwatunan gawa, yayin da malaman addinin kirista ke tsaye suna addu'a, sauran mutanen gari kuma na gefe suna kallo.

Haka nan akwai wasu hotunan da suka nuna yadda aka jera akwatunan a cikin wani makeken kabari.

Kaduna na cikin jihohin da suka daɗe suna fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga a tsakiya da kuma arewacin jihar, yayin da yankin kudancin jihar ke fama da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci.

Rikice-rikice irin wannan sun haifar da mummunar asarar rayuka a jihar wadda ke da mutane daga ƙabilu da addinai daban-daban.

Kimanin sama da shekara ɗaya da ta gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta shiga wata yarjejeniyar sulhu tsakanin al'umma da ƴan fashin daji a yankin Birnin Gwari mai fama da hare-hare.

Matsalar tsaro ta kasance kan gaba cikin abubuwan da suka fi ajalin mutane a Najeriya.

Rikice-rikice, kama daga na ƴanbindiga masu ɗauke da makamai zuwa faɗan ƙabilanci na daga cikin abubuwan da ke janyo mace-mace a ƙasar, da ke zaman giwar Afirka.

A baya-bayan nan gwamnonin arewacin Najeriya - yankin da ya fi fama da matsalar tsaro a ƙasar - suka yanke shawarar kafa wata gidauniyar yaƙi da matsalar.

Sun sha alwashin bayar da gudumawar kudi kowane wata a matsayin guduwa domin yaƙi da matsalar.

Gwamnatin Najeriya, wadda ita ce ke iko da jami'an sojoji da na ƴansanda ta sha ƙaddamar da shirye-shiryen yaƙi da matsalar amma abin ya ci tura.

Mahar na shiga ƙauyuka suna kashe mutane da kuma garkuwa da wasu domin neman kudin fansa, lamarin da ya durƙusar da lamurran noma da tattalin arzikin al'ummar yankin.